Iftila’in da ya faru da tsohuwar jaruma Maryam Wazeery “Lailah labarina” da Mijinta
Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji'un!!!
Tsohuwar jaruma a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Musa Waziri wadda ke amsa sunan Laila Masu Gonar Naira a tsohon shirin mu na Labarina Series da ya gabata, ta gamu da mummunar hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya tare da mijinta, Tijjani Babangida wadda tsohon dan wasan kwallon kafar Najeriya ne, da d'an ta Muhammad Fadeel
Kanin mijinta, Ibrahim Babangida, shi ya ke tuka motar da su ke ciki lokacin da hatsarin ya faru, wadda kuma a take Allah Ya karbi rayuwar sa, in da aka garzaya da ita kuma Maryma da d'anta da mijinta zuwa Asibiti don kula da lafiyar su.
Sai dai kwana daya da hatsarin, Allah Ya yi wa karamin d'anta, Fadeel rasuwa shima sakamakon buguwar da ya yi.
A yanzu haka dai a cikin mutum 4 da su ka yi hatsarin, Maryam da mijinta ne su ka saura, in da su ke karbar magani a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Shika a Zariya.
Daga cikin abun da wannan hatsari ya jawowa Maryam dai shine rasa bangare daya na fuskar ta:
Ta rasa ido daya
Ta rasa kunne daya
Hancin ta ya gutsire
Bakin ta ma ya gutsire
Da fatan Allah Ya jikan Ibrahim da Fadeel, Ya gafarta musu. Ya bawa Maryam da Tijjani Babangida lafiya. Amin.
Ga videon TVC


0 Comments