![]() |
Ma’aikaciyar jinya Ta fadi, ta mutu a bakin aiki Zamfara
Ma’aikaciyar jinya da ke aiki a Asibitin Ahmed Sani Yariman Bakura da ke Gusau a Jihar Zamfara, Asamau Lawali ta mutu kwatsam a yayin da take gudanar da ayyukanta a asibitin a yau laraba.
Rahotanni sun ce marigayiya Asma’u Bungudu ta kasance cikin bacin rai a lokacin da ta fito bakin aiki da sanyin safiyar Laraba, amma an tabbatar da rasuwarta a wasu sa’o’i da ta ci gaba da aikin.
Jami’in hulda da jama’a na asibitin kwararru na Ahmed sani Yarima, Auwal Usman ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ma’aikaciyar jinya Asmau tana ofishinta (NHIS Clinic) kuma ta duba majinyata kusan 30 a yau kafin ta kai kanta ga Likita game da ciwon zuciya da ke damunta .
A cewarsa, Marigayir ma’aikaciyar jinya Asma’u ta bayyana ma likitocin abunda da ke da munta su kuma basuyi kasa a gwiwa ba , likitoci suka yi gaggawar ceto ta amma nan take abun yaci tura tace ga garinku nan.
Jami'an hulda da Jama'a na Asibitin ya bayyana cewa tawagar gudanarwar asibitin karkashin jagorancin Daraktan Likitoci Dr Usman Muhammad Shanawa sun mika gawar ga ‘yan uwan ma’aikaciyar jinya da ta rasu.
Wata ‘yar gidan marigayiya Asma’u ta tabbatar da cewa Asmau ta bar gida cikin walwala a safiyar yau kuma ta tafi asibiti inda take aikin jinya.
"Anyi sallar jana'izarta yau da karfe 5:00 na yamma a gidan Malan Abdurrahaman dake unguwar Magama a garin Bungudu

0 Comments