CIKAKKEN BAYANI AKAN PELVIC INFLAMMATORY DISEASE (PID)CUTAR DAKE ADDABAR BANGAREN MAHAIFA.
PELVIC INFLAMMATORY DISEASE (PID) CUTAR DAKE ADDABAR BANGAREN MAHAIFA:
PID : Wata cutace wacce dake addabar bangaren da ya shafi mahaifar mace, da dama a nahiyan africa suna fama da wannan ciwon mussaman Nigeria.
Wassu kwayayoyin cututtuka né idan sun samu sun shiga mahaifar mace (Uterus, fallopian Tubes, ovaries or cervix ) sai ta haifar da Cutan PID.
DAGA CIKIN ALAMOMIN TA AKWAI:
1- Ciwon Qasan cibi (Ciwon mara).
2- fitar da ruwa mai wari a gaban mace.
3- Ganin jini a gaban mace musamman lokocin jima'i da bayan jima'i.
4- Zafi lokocin jima'i.
5- Zazzabi da jin sanyi.
6- Zafi lokocin fitsari ko wahalar fitsari.
7- Kaikayin gaba.
8- Rashin Daidaitawar jinin Haila.
9- Tashin Zuciya
10- Ciwo lokocin jima'i
11- ciwon baya
12- Zazzabi da Ciwon Kai.
Wasu lokutan harda amai kamar Alamomin Mai laulayi.
HANYOYIN DA'AKE DAUKAR WANNAN CIWO:
1- Jima'i da namiji mai dauke da cutar gonorrhea ko clamyadia
2- Amfani da kayan karban haihuwa wanda tsafta bai ishe su ba.
3- Yawan kai dan yatsa cikin farji.
4- Amfani ni da wando (Pant) wanda mai dauke da wannan cutar tayi amfani dashi.
5- Rashin amfani da condom lokocin jima'i ga Mai Ciwon sanyi.
6- Yawan tsaftace gaba da sabulu musamman masu dauke da sinadaran kashe kwayoyin cuta.
7- Yawan amfani da maganin kashe kwayoyin cuta erin su Ampiclox da muka dabi'untu da shan su kullum.
8- Yawaitar yin Bari ko yin wankin Mara akai akai.
PID: ldan ba'a magance shi da wuri ba tana kawo wadannan Matsalolin:
1- Rashin Haihuwa
2- Zaman ciki wajen mahaifan (Ectopic pregnancy)
3- Yakan kawo Yawaitar Bari ( Abotion ko Miscarriage)
4- Ciwon mara da baya mara jin magani.
5- Yawaitar Qaranchin Jini.
HANYOYIN KARIYA DAGA WANAN CIWON SUN HADA DA:
1- Amfani da Condom lokocin jima'i yana rage yaduwar PID kashi 95%
2- Mace tasaya akan namiji guda daya kuma a tabbata anyi gwaji kafin saduwa ko suyi aure.
3- A kiyaye Yawan saka hannu a farji.
4- A tsaftace wandon sakawa musamman pant , kuma a kiyaye amfani da pant na wata.
5- Adinga tsaftace Kayan karbar haihuwa da kuma wankin ciki.
WANNAN CIWO NA PID YANADA MAGANI IDAN AKABI HANYOYI MASU KAYU;
1- Da Zaran Mace taga alamun da muka lissafa a sama ta gaggauta zuwa asibiti.
Daganan Likita zaiyi gwaje gwaje da ya kamata a ayi antabbata menene matsalar sannan su bada magani.
2- Idan kina da miji shima ya kamata yaje a gwada shi abaku magani tare.
3- Daga nan sai a Kaurecewa Jima'i sai Likita ya tabbata muku kun warke.
GARGADI :
Idan mace tana tareda wannan cutar kuma tayi shiru ta zauna Sabida kunya ko makamancin haka yakan jawo mata matsala a mahaifarta daga nan zata fara gamawa da matsalar Zubar da ciki (miscarriage) zaman ciki wajen mahaifa (Ectopic pregnancy) ko samun qarin mahaifa(Fibroid) ko kuma rashin daukan ciki gabaki daya (Total Infertility).
ALLAH UBANGIJI YA BAMU LAPIA DA ZAMAN LAPIA AMIN YARAB.
Ga cikakken bayanin likita game da cutar P.I.D

0 Comments