Ad Code

Responsive Advertisement

Matar Aure Ta Shiga Ɗimuwa Bayan Ta Samu Junabiyu Da Direbanta

 Matar Aure Ta Shiga Ɗimuwa Bayan Ta Samu Junabiyu Da Direbanta.


Cikin wani labari mai cike da al’ajabi, wata matar aure ƴar kasar Ghana ta bayyana yadda ta ci amanar mijinta da direbanta wanda yanzu haka shine uban ƴaƴanta.

Bayan ta kasa samun sukuni bisa abinda ta aikata, matar auren ta tonawa kan ta asiri inda ta bayyana yadda ta samu juna biyu sau biyu tare da direbanta.


Da take bayyana abinda ya faru, matar auren wacce aka sakaya sunan ta, tace aurenta da mijinta ya kai shekaru shida, amma bata samu juna biyu ba.

Hakanne yasa ta yanke shawarar zuwa ganin likita wanda yayi mata gwaje-gwaje inda ya gaya mata cewa babu wata matsala a tattare da ita.


Sai dai shi mijinta yaki zuwa wajen likitan domin a duba lafiyar sa.

Ta ci amanar aure tare da direbanta

Da take cigaba da bayar da labarin nata mai matukar kaduwa, matar auren ta bayyana cewa sai ta fara sakarwa direbanta fuska wanda ta bayyana shi a matsayin mutumin kirki.




Bayan alaka ta kullu a tsakanin su, sai suka bige da yin lalata da juna inda har ta samu ciki. Bayan ta haifi yaron farko, ta kara samun wani juna biyun tare da direban nata inda ta haifi yaro na biyu.


Matar auren ta bayyana cewa direban ya san cewa yaran guda biyu na shine. Sai dai a daya bangaren kuma, mijin matar bai san cewa yaran banasa bane.


Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su akan abunda matar auren ta aikata


“sai dai lokacin da labarin abun ya samu mijin nata ya bayyana cewa zai rike yayan ya kula da su kamar ƴaƴansa daya haifa. kamar yanda wasu mutane suke dauko wasu yara su rike a matsayin yaran da suka Haifa.



Post a Comment

0 Comments