Ad Code

Responsive Advertisement

YOGOT NA WAKEN SOYA

 YOGOT NA WAKEN SOYA



Abubuwan da zaa nema

Waken soya 

Fresh me dandanon kwakwa

flebo me kamshin Madara Amma na ruwa


Yadda ake hadawa za,a gyara waken soya awanke akai markade Kamar na awarar in an dawo daga markade a tace Amma kar asanya manja ko wani Abu cikin Tatar sai azuba ruwan da aka tace cikin tukunya Amma tukunyar ta kasance me nauyi domin gudun kamawa,bayan an Dora Akan wuta zaa barshi ya tafasa sosai har gafin waken ya fita sai a sauke ajuye cikin babbar roba sai adan barshi ya Dan huce zafin ya ragu sai ananya murfi arufe robar ruf kar iska ta shiga zaa Kai waje me dumi a sanya ko bargo arufe sosai idan da daddare akayi zuwa safe zakiga ikon Allah kina budewa Zaki ga gaba daya ya daskare Kamar nono kindirmo haka Zaki sanya ludayi kina saroshi harki gama sannan ki burgeshi sosai ke da kanki zakiga kamar YOGOT din kanti sai asanya rariya a tace a kawo fresh na kwakwa da Kuma milk flebo Amma na ruwa domin shine yake bada kamshin YOGOT sak sai azuba daidai dandanon da kike ganin costumers dinki zasu shikenan kin ksmmala YOGOT ke dakanki idan kinsha zakiji gardi da dadin YOGOT din Zaki iya Kara ruwa daidai kaaurin da kike bukata domin yanada auki daganan saiki dura agoruna ya danganta da inda kike sayarwa naira dari ko hamsin ko Kuma ki sayo robobi irin na YOGOT ki dura kiyi sitika da sunan kamfanin ki ki fara kaiwa Yan kasuwa makarantu ko awajan aiki makota da sauran su ,wannan sanaar tanada riba Kuma Bata bukatar jari Mai yawa.

Ayi sharing don Allah 

Post a Comment

0 Comments