Ad Code

Responsive Advertisement

DAMBUN SHINKAFA DA UGU

 DAMBUN SHINKAFA DA UGU




Shinkafa

Ganyen ugu

Albasa

Maggi fari

Gishiri


Dama kin wanke barzajjiyar shinkafarki kin ajiye gefe daya, ki wanke ganyen ugun tare da gishiri sai ki yanka shi ki sake wankewa da fan gishiri ki tsane shi a kwando,sai ki yanka albasa,kizo ki saka gishiri da farin maggi akan shinkafar ki juya su hade jikinsu ki kawo ganyenki ki zuba ki juya su har sai sun hade jikinsu Sai ki tirarata a madambaci,idan ya tirara kamar 30min

saiki sauke ki juye a mazubi mai fadi ki juya shi sosai domin ya kara hade jikinsa,idan yana da karfi zaki iya kara yayyafa masa ruwa akai ki juya Sai ki mayar kan wuta a madambacin ki rife ya karasa dahuwa zaki ji kamshinsa ya soma tashi kuma yayi laushi saiki sauke ,shikenan kin kammala DAMBUN SHINKAFA MAI UGU Sai serving da mai da yaji ko kuma sauce kamar yanda zan ci nawa da sauce In shaa Allah.


Note-

Ko kinsan zaki iya yanka ganyen ugu ki shanya a inuwa ya bude saboda amfanin gaba?

Hakan nake Yi wasu lokutan,shine kuke Gani a faranti guda2 na shanya a daki.


Post a Comment

0 Comments