Ad Code

Responsive Advertisement

Wata Yar Najeriya Ta Sharɓi Kuka A Bidiyo Mai Ratsa Zuciya, Ta Ce Ta Gaji Da Aiki A Dubai

 Wata Yar Najeriya Ta Sharɓi Kuka A Bidiyo Mai Ratsa Zuciya, Ta Ce Ta Gaji Da Aiki A Dubai.


Wata budurwa yar Najeriya da ke aiki a Dubai ta koka kan cewa ta gaji da aiki a kasar a kafar sada zumunta.

A wani bidiyo da ta wallafa a TikTok da aka yi imanin a wurin aiki ta dauka, budurwar ta yi kuka a bidiyon, tana juyayin yadda za ta fada wa mahaifiyarta yadda ta ke ji game da aikin

Da ta ke mayar da martani ga masu amfani da shafukan intanet, ta bayyana cewa ta shafe kimanin shekaru hudu a Hadaddiyar Daular ta Laraba. Amma, ba ta fayyace irin aikin da ta ke yi ba.


Bidiyon na ta na TikTok ya yadu, inda mutane da dama suka karfafa mata gwiwa kada ta karaya. Wasu sun sa ta fahimci cewa ta fi wasu da ke Dubai din na watanni amma ba su da aiki.


Kalli bidiyon a nan 👉👉👉 FULL VIDEO.







Post a Comment

0 Comments